BUHARI YA AMINCE DA FITAR DA BILIYAN N10BN DOMIN TALLAFAWA MUTANEN FILATO DA RIKICI YA SHAFA
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana iftila’in gobarar
tankar dakon man fetur da ya faru a Legas a mastayin daya daga cikin manyan
annoba da suka faru a Najeriya a baya-bayan nan.
Shugaban kasar ya bayyana haka ne cikin wani jawabi da
kakakinsa, Malam Garba Shehu, ya raba ga manema labarai a Abuja. Buhari ya
bayyana cewar lamarin ya matukar girgiza shi da nuna alhininsa bisa asarar
rayuka da dukiya da gobarar ta haifar.
Da yammacin yau Alhamis ne wata babbar motar tanka ta kama da
wuta a gadar Otedola dake wajen jihar Lagas, a kan babbar hanyar zuwa Ibadan.
Rahotanni sun bayyana cewa hukumar bayar da agajin gaggawa ta
jihar Legas (LASEMA) da hukumar kashe gobara ta jihar sun gaggauta zuwa wurin
da abin ya afku. Kazalika rundunar ‘yan sanda ta ko-ta-kwana (RRS) ta ce ta
tura jami’anta domin shawo kan lamarin. Saidai karfin wutar ya yiwa gaske
saboda kasancewar motar na dauke ne da man fetur, sannan motocin dake kusa da
wurin suma duk sun kama da wuta. A cewar shaidu da abun ya afku a idanunsu,
sunce wutar ta lashe sama da motoci 20 da kuma wasu mutane da ba’a san adadinsu
ba akan gadar ta Otedola dake kan babban titin Legas zuwa Ibadan.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku