ABINDA BUHARI DA LALONG SUKA FADAWA JAMA'AR FILATO
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta kawo karshen
matsalolin tsaro da ake fama dasu saboda ya san dukkan matsalolin da ke adabar
kasar tun kafin ya tsaya takarar shugabancin kasar.
Shugaban kasar ya furta wannan magana ne a ranar Talata a
gidan gwamnati yayin da ya ke jajintawa mutanen da aka kaiwa hari a
Barikinladi, Riyom da wasu sassan kudancin Jos inda aka rasa rayyuka masu yawa.
"Na yi takarar shugababancin kasa har sau hudu kafin nayi nasara saboda
haka ba zan iya yin korafi kan matsalolin da ake adabar Najeriya ba," inji
shugaba Buhari.
Shugaban kasar ya cigaba da cewa gwamnatinsa da samu nasarori
sosai a fanin samar da tsaro a kasar.

"Babu wanda zai iya cewa bamu tabuka komai ba a fanin
samar da tsaro, munyi iya kokarinmu amma a halin yanzu abinda za mu iya yi
shine addu'a," inji shugaban kasan. Ya kuma yi kira da dukkan shugabani su
zage damtse wajen gabatar da ayyukansu ga al'ummar yankunansu. A bangarensa,
gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya yi ikirarin cewa wasu bata gari ne da ke
son tayar da fitina ne suka kai harin saboda suna son tayar da rikici a
jihar," inji shi. Gwamnan ya ce wasu mutane a jihar suna kokarin alakanta
harin da addini musamman a Barikin ladi. Gwamnan ya ce gwamnatinsa ba za tayi
kasa a gwiwa ba wajen tsare lafiya da dukiyoyin al'umma a Jihar.
Gwamna Lalong ya yi ikirarin cewa wadanda suka kawo harin
baki ne daga kasashen ketare. "Bisa ga dukkan alamu irin makaman da akayi
amfani dasu wajen kai harin ba suyi kama da irin makaman da ake amfani dasu
wajen kare kai ba a kasar mu, hakan yasa muke tunanin wasu daga kasashen waje
ne suka kawo harin," inji Lalong.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku