"YA KAMATA INEC TA HARAMTA WA APC TAKARA A ZAMFARA"

Jam’iyyun adawa a jihar Zamfara da ke tarayyar Najeriya, sun bukaci hukumar zabe, INEC da ta shelanta cewa, jam’iyyar APC mai mulki a jihar ba ta da ‘yan takara a zabuka masu zuwa, saboda a cewarsu jam’iyyar ta gaza gudanar da zabukan fid da gwani kafin ranar 7 ga watan Oktoba kamar yadda ka’idojin zabe suka shata.



A hirarsa da sashen hausa na RFI, Alhaji Sa’idu Muhammad Dansadau, shugaban Jam’iyyar National Rescue Movement wadda suke kira da Jam’iyyar Ceton Al’umma na kasa kuma dan takarar gwamna a jihar, ya ce tuni suka sanar da hukumar zabe a hukumance dangane da haka.
Dansadau ya ce, dokokin Najeriya sun bukaci haramta wa wata jam’iyya shiga takarar zabe muddin ta gaza gudanar da zaben fid da gwani.
Kuna iya latsa alamar sauti da ke kasa don sauraron muryar Alhaji Dansadau.

DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA  

Comments