ZABEN NAJERIYA: SARKIN MUSULMI YA JA HANKALUN SHUGABANNIN ADDINAI



Mai alfarma Sarkin Musulmi a Najeriya Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bukaci shugabannin addinai da su ja hankulan mabiyansu domin kaucewa tashin hankali musamman ma a daidai lokacin da kasar ke shirye-shiryen gudanar da zabubuka.
Sarkin Musulmi na wannan kira ne a lokacin da yake ganawa da tawagar manyan limaman cocin Katolika da suka ziyarce shi a birnin Sokoto ranar juma’a.
Muhammad Sa’ad Abubakar ya ce ‘lokaci ya yi da ya kamata a gaya wa juna gaskiya a Najeriya, domin kuwa akwai abubuwan da ba sa tafiya daidai a kasar, sakamakon yadda jama’a ke fakewa da addini ko kabilanci domin biyan bukatunsu musamman a irin wannan yanayi na siyasa’.



DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA  
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com


Comments