MASARAUTAR KANO NA GAB DA FITAR DA DOKAR MUTUWAR AURE
Masarautar
Kano a Najeriya na aiki tukuru kan wani kudirin doka da zai magance matsalar
yawaitar mutuwar aure tare da tilasta wa magidanta daukan cikakkiyar dawainiyar
iyalansu.
Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu
Sunusi na II ya bayyana haka a yayin ganawa da manema labarai a gefen wani taro
da Asusun Tallafawa al’umma na Majalisar Dinkin Duniya ya shirya a birnin
Abuja.
Sarkin wanda Talban Kano ya
wakilce sa, ya ce, Masarautar ba za ta lamunce wa maza sakin matansu ba tare da
daukan hidimar kulawa da yaransu ba.
Nan kusa za kwamitin da ke
aiki kan kudirin dokar zai kammala aikinsa kafin gabatar da shi ga Majalisar
Dokokin Jihar don amincewa da shi a matsayin doka.
Kwamitin ya kunshi manyan
alkalai da malaman addinin Islama da malaman ilimin zamani na boko.
Ana sa ran dokar za ta taka
muhimmiyar rawa wajen rage raragaitar kananan yara a kan titunan jihar matukar
gwamnati ta amice da ita.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku