JIHOHIN NAJERIYA NA FUSKANTAR IFTILA'IN AMBALIYAR RUWA - INJI NEMA


Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta shelanta cewa jihohin Kogi, Niger, Delta da kuma Anambra na fuskantar Iftila’in ambaliyar ruwa fiye da sauran takwarorinsu a kasar.
Babban darakatan hukumar ta NEMA Mustapha Maihaja ne ya sanar da daukar matakin, wadda ya ce umarni ne daga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.


Daraktan ya kuma ce tuni hukumar ta NEMA ta sa idanu akan wasu jihohin guda takwas da suma ke fuskantar ambaliyar ruwan a sassansu, domin bibiyar halin da ake ciki.

Yayin da yake yiwa Bashir Ibrahim Idris na RFI Hausa karin bayani kan halin da ake ciki ta wayar tarho, Maihaja, ya ce daukar matakin ya biyo bayan ziyarar gani da ido da suka kai zuwa wasu sassan da iftila’in ya ya aukawa



Sai dai a cewar babban jami’in na NEMA, daya daga cikin kalubalen da suke fuskanta shi ne rashin samun hadin kan wasu daga cikin wadanda ake kokarin ceto su daga hallaka.



 DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA  

FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  

Comments