HUKUMAR 'YAN SANDA TA NAJERIYA TA HANA KARIN GIRMA GA MASU KATON TUMBI
Hukumar Kula da ‘Yan kasa ta
Najeriya ta koka yadda akasarin ‘yan sandan kasar ake samunsu da katon tumbi
saboda rashin motsa jiki.
Daga yanzu Hukumar ta ce duk
wani dan sanda mai katon tumbi to kuwa shi da samun Karin girma saidai ya hangi
wasu an yi masu.
Majiyar Naij.com ta ce a cikin Wata sanarwa daga Hukumar na
cewa bayaga neman kowa ya rage girman tumbinsa dole ne masu bukatan samun Karin
girma su yi nasarar cin jarabawa da ake yi masu.
Sanarwar na cewa Shugaban
Hukumar kula da 'yan sanda Musliu Smith ya damu matuka da yadda ake
yawaitan sauyawa wasu ‘yan sanda wuraren aiki maimakon a bar mutun ya yi akalla
shekaru biyu zuwa uku.
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku