GANAWAR MANYAN JAMI'AN APC DA TSOHON GWAMNAN KANO SHEKARAU
Shugaban jam’iyyar APC mai
mulki a Najeriya Adams Oshiomhole, ya ce ganawarsu jiya juma’a da tsohon
gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekaru wanda jigo ne a jam’iyyar PDP mai
adawa ta yi armashi.
Oshiomhole wanda ke tare da
rakiyar gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da kuma wasu kusoshin jam’iyyar
APC, sun gana da Shekarau ne a birnin Kano kwanaki kadan bayan da wani na
hannun damansa ya ce tsohon gwamnan ya canza sheka daga PDP zuwa APC, labarin
da daga bisani ya musanta da kansa.
Wasu majiyoyi sun ce a
lokacin ganawar, jam’iyyar APC ta yi wa tsohon gwamna Shekarau alkawarin ba shi
tikitin tsayawa takarar kujerar dan majalisar dattawa da ke wakiltar Kano ta
tsakiya, wadda ita ce mazabar tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso, yayin da wasu
bayanai ke cewa abu ne mai yiyuwa gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bai wa makusanta
Shekarau mukamai a cikin gwamnatinsa nan gaba.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku