DANDALIN KANNYWOOD: GASKIYAR ALAKA TA DA ADAM A. ZANGO - ZAINAB INDOMIE
-
Zainab Indomie ta fadi me ke tsakanin ta da Adam Zango
-
Tace ya taimake ta sosai
-
Tace ta dauke shi a matsayin dan uwa
Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar
Kannywood watau Zainab Abdullahi da aka fi sani da Zainab Indomie ta bayyana
ainihin alakar ta da jarumi, Adam A. Zango.
Jarumar dai wadda yanzu haka ta sanar da dawowar ta harkokin
fina-finai ta ce ita ta dauki Adamu a matsayin ubangida a gare ta da har zata
iya kiran sa dan uwa amma babu zancen soyayya a tsakanin su. Zainab Indomie ta
kara da cewa: "Zango ya na taimaka min sosai, musamman don ganin na cimma
nasara a wannan sana'a".
wannan dai na zuwa ne a lokacin da ake ta rade-raden cewa
jaruman suna shirin yin aure ne sakamakon soyayyar dake tsakanin su musamman ma
bayan da Adam Zango din ya saki matar sa. Ita dai Zainab Indomie, kamar yadda
masoyanta da ma'abota fina-finan Hausa suka fi sanin ta, ta yi fice a
masana'antar Kannywood a shekarun baya musamman sakamakon irin rawar da ta taka
a wasu manyan fina-finai. Daga cikin fina-finan da suka sanya jarumar ta
shahara akwai 'Wali-Jam', da 'Ali' da 'Garinmu Da Zafi' da sauransu.
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku