CUTAR KWALARA TA HALLAKA MUTANE 55 A JAMHURIYYAR NIJAR



Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin ci gaba da yaduwar cutar Kwalara a Jamhuriyyar Nijar, bayan da wasu alkaluma ke nuna yadda cutar ta hallaka akalla mutane 55 daga watan Yuli zuwa Satumba.
Majalisar ta ce yanayin yadda cutar ke yaduwa daga yankunan da aka fara samun bullarta zuwa wasu yankunan na daban na nuni da cewa akwai bukatar daukar kwararan matakan yakarta.
Hukumar kula da ayyukan jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA a kididdigar da ta fitar bayan binciken da ta gudanar a Jamhuriyyar ta Nijar ta ce daga watan Yuli zuwa 10 ga watan Satumbar da mu ke ciki akalla mutane 55 suka mutu sanadiyyar cutar yayinda wasu dubu 2 da 752 kuma suka kamu da ita.
A cewar hukumar ta OCHA cutar wadda ta faro daga Madarumfa cikin watan Yuli yanzu haka ta watsu a wasu sassa na Dosso da Tahoua da kuma Zinder.
Hukumar ta yi gargadin cewa matukar ba a dauki kwararan matakan yakar cutar ba, babu shakka za ta iya yin illar da ba a yi tunani ba, la’akari da saurin kisan da ta ke ci gaba da yi daga mutane 22 a Yuli zuwa 55 a farkon watan Satumba.

DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA  


Comments