Sunday, September 2, 2018

ADADIN SOJOJIN DA BOKO HARAM SUKA KASHE YA KARU

- A jiya, Asabar, ne mayakan kungiyar Boko Haram suka kai hari wani sansanin soji a jihar Borno 
- Ana zargin cewar mayakan sun kashe manyan sojoji biyu da kananan sojoji 50 
- Hukumar sojin Najeriya ta musanta rahotannin kai harin tare da musanta adadin wadanda suka mutu 



An gano karin gawarwakin dakarun sojin Najeriya 17 da suka rasa rayukansu yayin fafatawarsu da mayakan boko haram a arewacin Maiduguri gab da kan iyakar Najeriyar da Jamhuriyyar Nijar, a wani hari da suka kai musu na yunkurin kwace iko da sansaninsu da ke garin Zari.

Jaridar Premium Times ta Najeriyar ta ruwaito yadda tawagar masu binciken gawarwakin sojin bayan rikicin na daren ranar Alhamis ta gano gawar wani Hafson soji guda da kuma kananan soji 16 cikin karshen makon nan a yankin karamar hukumar Mobbar.

Tun a daren ranar Alhamis ne wani adadi mai yawa na mayakan boko haram ya dirarwa sansanin sojin najeriyar da ke kauyen Zari gab da iyakar Nijar inda bayan fafatawa mayakan suka hallaka tarin jami’an baya ga jikkata wasu da dama.

Yanzu haka dai dakaru na musamman daga Bataliyar sojin Najeriyar ta 145 na ci gaba da aikin lalubo wadanda suka bace bayan harin yayinda su ke aikewa da gawarwakin da suka gano zuwa garin Maiduguri.


DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA  

No comments:

Post a Comment

Ku bada ra'ayoyin ku