2019: DAVID MARK DALILIN DA YASA YA KE SON ZAMA SHUGABAN KASA
-
Sanata David Mark ya shiga sahun masu neman tikitin takarar shugabancin kasa a
jam'iyyar PDP
- David Mark ya ce daya daga cikin abinda da
yasa ya ke son zama shugaban kasa shine canja fasalin Najeriya
- Ya kuma lissafo wasu muhimman dalilai a
karkashin tsarinsa na musamman mai taken '730'
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David
Marki ya bayyana dalilan da yasa ya shiga sahun masu neman takarar zama
shugaban kasa a Najeriya. David Marki, wanda ke waliktan mazabar Kudancin
Benue, ya siya tikitin takararsa ne a sakatariyar jam'iyyar PDP da ke Abuja a
yau Talata. Dan majalisar da yafi kowa dade wa a majalisar ya lissafo wasu
dalilai da ya sanya shi shiga takarar shugabancin kasar a karkashin inuwar jam'iyyar
PDP.
"Duk
da irin banbance-banbancen siyasarmu, babu shaka lokaci ya yi da ya kamata a
fuskanci batun sake fasalin Najeriya," kamar yadda David Mark
ya fadi a wata sako mai dauke da sa hannun mai taimaka masa a fannin yada
labarai.
"Nayi
imanin cewa sake fasalin zai karfafa zumunci tsakaninmu da hadin kai saboda
babu wanda zai rika ganin kamar an mayar da shi saniyan ware kuma mutane za su
iya zama a kowanne yanki a kasar ba tare da fargaba ko cin fuska ba." Inji
shi
Mark ya gabatar da wasu tsatsare da ya yiwa
take da '730' wadanda ya ke ganin za su magance matsalolin Najeriya cikin
shekaru biyu. Ya yi alkawarin kawar da talauci, samar da ayyukan yi wanda hakan
yasa matasan Najeriya ke jefa rayuwarsu cikin hadari a Teku ko Sahara a
yunkurinsu na zuwa kasashen waje domin samun ayyukan yi. Ya kuma ce zai mayar
da hankali wjen bayar da tallafi ga masu kananan masana'antu ta hanyar basu
bashi mara ruwa saboda su samar da fasahar da za ta bunkasa tattalin arzikin
Najeriya da samar da ayyukan yi.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku