TRUMP YA BAYYANA BUHARI DA RASHIN KARSASHI




Jaridar Financial Times da ke kan gaba wajen wallafa labaran harkokin kasuwanci a duniya, ta rawaito cewa, shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana ganawar da ya yi da takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari a cikin watan Afrilu a matsayin mara karsashi, yayin da ya gargadi mukarrabansa cewa, ba ya fatan sake ganawa da mutum mara kuzari.
Buhari ya kasance shugaba na farko daga yankin Afrika da ke Kudu da shahara da ya ziyarci fadar White House a ranar 30 ga watan Afrilu don tattaunawa da Trump kan batutuwan tsaro da tattalin arziki da kasuwanci da zuba jari da kuma salon shugabanci.
Sai dai a cewar jaridar, shugabannin biyu sun kammala taron tare da wani gargadi da ya fito daga Trump da ke cewa, ba ya fatan sake ganawa da mutum mara karsashi.
Kawo yanzu fadar shugaban Najeriya ba ta mayar da martani ba kan batun duk da cewa Trump ya jinjina wa Buhari a bainal jama'a a yayin taron manema labarai da suka gudanar tare a wancan lokacin a Washington.
Wannan na zuwa ne a yayin da shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ke shirin ganawa da Trump a yau Litinin a fadar White House, yayin da jaridar ta Financial Times ta kara da cewa, ana fatan ganawarsu ta yau ta farfado da dangantaka tsakanin Amurka da yankin Afrika.

DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 


Comments