TAKAITACCEN TARIHIN MARIGAYI KOFI ANNAN



A binciken da majiyar mu ta yi game da rayuwar tsohon shugaban majalisar dinkin duniya MDD, marigayi Mr Kofi Annan, za mu kawo muku takaitaccen tarihin rayuwar shi da kuma muhimman mukaman da ya rike a rayuwar shi.

A binciken da majiyar mu ta yi game da rayuwar tsohon shugaban majalisar dinkin duniya MDD, marigayi Mr Kofi Annan, za mu kawo muku takaitaccen tarihin rayuwar shi da kuma muhimman mukaman da ya rike a rayuwar shi.

Tarihi ya nuna cewar marigayi Kofi Annan shine bakin mutum dan Afirka na farko da ya fara rike shugabancin majalisar dinkin duniya.

08-04-1938: An haifi marigayi Kofi Annan a kasar Ghana a birnin Kumasi, ya fito daga yaren Fante.

1962: Bayan yayi karatu a fannin tattalin arziki a Geneva, ya fara aiki da hukumar lafiya ta duniya, inda daga nan ya cigaba da aiki da wasu bangarori na majalisar dinkin duniya, ciki harda bangaren 'yan gudun hijira na majalisar.

1972: Marigayi Kofi Annan ya kammala karatun sa na digiri na biyu a jami'ar kimiyya da fasaha ta Massachusetts.

1993-96: Ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban masu kawo zaman lafiya na majalisar dinkin duniya, a lokacin da aka yiwa mutanen Rwanda kisan kare dangi da kuma yakin kasar Bosnia.

01-01-1997: Ya zama sakataren majalisar dinkin duniya, sannan na farko a yankin nahiyar Afirka. Sannan an kara zabar shi a karo na biyu a watan Yuli na shekarar 2001.

12-10-2001: An bashi kyautar 'Nobel Peace Prize' tare da majalisar dinkin duniya.

2005: Ya shiga cikin badakalar cin hanci da rashawa na majalisar dinkin duniya a fannin tsarin da majalisar ta shirya na abinci a kasar Iraq. Sai dai daga baya an zo an wanke shi daga zargin da ake yi mashi.

2007: Ya zama daya daga cikin wanda suka assasa kungiyar manyan masu fada aji a duniya. Sannan ya fito da kungiyar 'Kofi Annan Foundation' wacce take kokarin ganin an gabatar da shugabanci na gari da kuma kawo zaman lafiya a duniya.

2012: Majalisar dinkin duniya tare da tarayyar Larabawa sun zabe shi a matsayin wanda zai sanya ido a yakin da ake yi a kasar Syria.

18-08-2018: Marigayi Kofi Annan ya bar duniya a kasar Switzerland, bayan yasha fama da jinya.


DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/

ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html

Comments