SULTAN YA AIKE DA SAKO NA MUSAMMAN GA MUSULMI A KAN WATAN DHUL HIJJAH
Mai alfarma sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar, ya
nemi musulmi da su fara duba sabon watan Dhul Hijjah daga yau, Lahadi, 12 ga
watan Agusta.
Sarkin Musulmin ya bayar da wannan umarni ne a
cikin wani sako da Farfesa Sambo Junaidu, shugaban kwamitin bayar da shawara a
kan harkokin addini, ya saka wa hannu yau a Sokoto.
"Muna sanar da al'ummar musulmi da su fara
duba sabon watan Dhul Hijjah daga yau Lahadi 12 ga watan Agusta wacce tayi
daidai da ranar 29 ga watan Dhul Qadah," a cewar sanarwar.
"Musulumi su fara duba watan domin sanarwa
dagatai ko hakimai dake kusa da su domin isar da sako ga mai alfarma sarkin
Musulmi," sanarwar ta kara da fadi. Kazalika ya yi addu'a ga Allah da ya
bawa musulmi ikon yin aiyuka na alheri.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku