SOJOJIN NAJERIYA SUN YI ZANGA-ZANGA A BORNO


Wasu daga cikin jami’an sojin Najeriya da ke cikin rundunar ‘Operation Lafiya Dole’ mai yaki da kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya sun yi bore a jiya Lahadi.




Sojojin wadanda yawansu ya kai kimanin 300, sun yi boren ne a filin jiragen sama da ke garin Maiduguri, inda suka rika harbin iska, abinda ya razana maniyyata aikin Hajjin bana dake shirin tashi.
Majiyar sojojin tace sun yi boren ne domin nuna rashin amincewar su da shirin tura su karamar hukumar Marte bayan sun kwashe shekaru kusan 4 suna yaki a Barno ba tare da sun je sun ganin iyalan su ba.
Daya daga cikin sojojin da ya nemi a sakaya sunan sa ya shaidawa wakilinmu a Maiduguri cewa, tun a ranar 2 ga watan Fabarairu na shekarar 2015 aka turasu jihar Borno, tare da akalla motoci 55, wadanda ya ce daga cikinsu kwaya uku ne kawai suka rage, sakamakon gwagwarmayar da suka fuskanta, wasu suka lalace yayinda wasu nakiyoyin da aka binne ya tarwatsa su.
A cewar jami’in sojon babbar bukatarsu shi ne basu isasshen lokacin hutu domin samun ganawa da iyalansu, da kuma murmurewa don sake samun karsashin komawa fagen daga, to amma hutun da ake basu baya wuce kwanaki 14.
A cewar sojin abin da ya fusata su shi ne yadda aka nemi a tura su Marte daga tsaron filin jiragen saman Maiduguri, inda za’a musanya su da wasu sojin da za a turo daga cikin birnin na Maiduguri.
Sai dai da safiyar yau Litinin, boren ya zo karshe, bayan da sabon shugaban rundunar ta Operation Lafiya Dole Manjo Janar Abba Dikko ya gana da sojojin da suka fusata.
Cikin sanawar da mataimakin kakakin rundunar ta Operation Lafiya Dole ya fitar, Kanal Onyema Nwachukwu, rundunar sojin Najeriyar ta ce za ta dauki matakan da suka dace wajen ganin ba a sake samun makamanciyar matsalar boren sojin ba.
Rundunar ta kuma bukaci jama’a da su kwantar da hankulansu la’akari da kawo karshen sabanin da aka samu.



DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/

ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html

Comments