SHUGABA BUHARI YA NUNA GOYON BAYAN SA DARI BISA DARI GA MAMA TARABA


- Shugaba Buhari ya nuna goyon bayan sa dari bisa dari ga tsohuwar 'yar takarar gwamnan jihar Taraba, Aisha Alhassan wacce aka fi sani da Mama Taraba

- Yayi alkawarin tabbatar da zabe cikin aminci da kwanciyar hankali a fadin kasar nan




A wata wasika da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikawa da tsohuwar 'yar takarar gwamnan jihar Taraba kuma ministar harkokin mata a yanzu, Hajiya Aisha Jummai Alhassan, shugaban kasar ya nuna goyon bayan shi dari bisa dari akan kokarin da take na sake fitowa takarar gwamnan jihar Taraba a karo na biyu.

Ga abinda shugaban kasar ya ce a wasikar tashi. 

"Na samu wasikar ki a yau da take nuna mini burin ki na sake fitowa takarar gwamnan jihar Taraba a karo na biyu. Bari nayi miki godiya a madadin dukkanin al'ummar Najeriya da irin kokarin da kika yi wurin bada lokacin ki wurin kawo cigaba ga wannan gwamnati. Na san irin kokarin da kika yiwa jam'iyyar APC a zaben da ya gabata na shekarar 2015. Kamar yanda kika sani, a halin yanzu hankalina ya koma kan tabbatar da cewar an yi zabe mai aminci a kasar nan. Sannan burin mu shine mu goyawa duk wani dan jam'iyyar APC baya domin ya samu nasara. Saboda haka ina yi miki fatan alkhairi a kokarin da kike na zama gwamnar jihar ki. Sannan ina tabbatar miki da cewar duk wata hukumar tsaro da ma'aikatu dama hukumar zabe ta kasa zasu samu goyon bayana dari bisa dari wurin gabatar da zabe cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali a shekarar 2019."

A shekarar 2015 dai Hajiya Aisha Alhassan ta taba fitowa takarar gwamnan jihar Taraba bata samu damar hayewa ba, to a wannan karon ma dai ta fito da niyyar tsayawa takarae gwamnan jihar.



DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/

ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html

Comments