SARAKI YA KARBI FOM DIN TAKARAR SHUGABAN KASA


Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya karbi fom din takarar shugaban kasa a ofishin jam’iyyar PDP.

Darektan kamfen din Saraki Mohammed Wakil, ne ya karba fom din a madadin Sa.
Idan ba a manta ba Saraki ya bayyana aniyar sa na takarar shugaban kasa jiya a wani taro a Otel din Sheraton dake Abuja.
Sauran ‘yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP sun hada da Rabiu Musa Kwankwaso, Ibrahim Sherau, Ahmed Makarfi, Ibrahim Dankwambo, Atiku Abubakar, Datti Baba-Ahmed, Sule Lamido, attahiru Bafarawa, Aminu Tambuwal da Tanimu Turaki.

DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA  


Comments