RUNDUNAR SOJI SUN KAWAR DA YAN BOKO HARAM 3 SUN KWATO MAKAMAI




Yan ta'addan Boko Haram sun sha gagarumin kaye yayinda sojojin Najeriya suka kai masu harin bazata harma an kashe uku daga cikin yan ta'addan. 



Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa tayi nasarar kawar da yan ta’addan Boko Haram uku a wani harin bazata a kauyen Mayanti dake karamar hukumar Bama na jihar Borno a ranar Juma’a, 24 ga watan Agusta. Birgediya Janar Texas Chukwu, daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya saki a Maiduguri a ranar Juma’a. Ya bayyana cewa rundunar bataliya 151 ne suka hallaka yan ta’addan.

Chukwu ya bayyana cewa an kwato makamai daga hannunsu wadanda suka hada da bindigar AK47, Mujalla uku, alburusai 32, babur daya da wayoyin android biyu.
Ya bayyana cewa ana kokarin kama sauran mambobin kungiyar yan ta’addan. 


Comments