OSINBAJO YA SALLAMI SHUGABAN HUKUMAR SSS DAGA BAKIN AIKI


Mukaddashin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya umarci shugaban gukumar tsaron sirri ta farin kaya DSS Lawal Daura ya ajje mukaminsa cikin sauri.





Osinbajo ta bakin wata sanarwa da kakakinsa Laolu Akande ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya umarci da ajje mukamin na Lawal Daura ba tare da bata lokaci ba.
Ana dai ganin matakin na sa na da nasaba da rawar da jami’an hukumar suka taka na mamaye majalisar Najeriyar a yau Talata.


DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/

ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html

Comments