NAJERIYA DA BIRTANIYA ZA SU INGANTA HARKAR KASUWANCI


Firaministan Birtaniya Theresa May ta sha alwashin inganta zuba jari da kuma dabbaka hada-hadar kasuwanci da Najeriya da zaran kasar ta fice daga cikin Kungiyar Kasashen Turai.




Uwargida May wadda ta samu rakiyar ministocinta da masu zuba jari da kuma tarin 'yan kasuwa, ta bayyana haka ne lokacin da ta gana da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a birnin Abuja.
Jim kadan da kammala ganawar, Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Geoffrey Enyeama ya shaida wa manema labarai cewa, shugabannin biyu sun sanya hannu kan yarjeniyoyi biyu da suka hada da tsaro da bunkasa tattalin arziki.
Wannan ziyarar na cikin shirye-shiryen gwamnatin Birtaniya na dabbaka alaka tsakaninta da kasashen duniya bayan ficewarta daga Kungiyar Tarayyar Turai

DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA  


Comments