MUTANE MILIYAN BIYU NE AKE SARAN ZASUJE AIKIN HAJJIN BANA
Hukumar Saudiya ta ce akalla mutane miliyan
Biyu ne daga fadin duniya ake sabran zasu hadu a birnin Makka dama garuruwan
dake makwaftaka dashi a birnin saudiya don gudanar da aikin Hajjin bana, wanda
za'a fara a ranar Lahadi.
Aikin Hajji, wanda yana daya daga cikin shika
shikan musulunci guda biyar, ya jaba akan kowane musulmi ya gudanar dashi koda
sau dayane a rayuwarsa madamar yana da halin yin hakan.
a'a kammala aikin hajjin ne a ranar Alhamis. A
yayin aikin Hajjin, maza na sanya fararen tufafi, yayin da suma mata ke sanya
fararen kaya (Harami) amma an haramta masu yin kwalliya da sanya sarkokin gwal.
Dukkan maza da matan na gudanar da aiki iri daya don samun haduwar kawunan
musulmi, da nuna rashin banbanci da kuma tuba daga laifukan da suka aikata.
A cewar alkaluman da hukumar Saudiya ta fitar,
sama da mutane 750 suka rasa rayukansu a wajen jifar Shaidan a garin Mina kusa
da Makka shekaru Uku da suka wuce. Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito
cewa a shekara ta 2017, mutane Miliyan 2.4 ne sukayi aikin Hajji. A cewar
rahotanninna alkaluman lissafi da kamfanin labarai na Al Jazeera ta wallafa,
kasar Masar mai mahajjata 108,000, itace kasar datafi yawan mahajjata a yankin
Africa a 2017, duk da cewa itace ta biyar a jadawalin sunayen.
Nigeria mai mutane 79,000 tazo ta 10 a
jadawalin sunayen kasashe a 2017, inda Iran ta biyo bayanta da kuma Turkiya.
Algeria nada mahajjata (36,000) yayin da Morocco keda (31,000).
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku