MENENE AMSAR TSAYAWAR SARAKI TAKARAR SHUGABAN KASA
Shugaban majalisar
dattijan Najeriya, Bukola Saraki, ya ce yana nazari taka takara a zaben
shugabancin kasar na 2019.
Saraki ya bayyana aniyar tasa ce a lokacin da
yake zantawa da kafar yada labarai ta ‘Bloomberg’ mai hedikwata a birnin New
York, inda ya ce yana da kwarin gwiwar zai iya kawo kyakkyawan sauyi a
al’amuran Najeriya.
Yayin da yake tsokaci akan datse kofar shiga
majalisun kasar da jami’an tsaron farin kaya na DSS suka yi, Saraki ya ce
kamata ya yi a ce ‘yan Najeriya sun damu matuka kan matakin, la’akari da cewa
ba’a hakan bait aba faruwa a tarihin kasar ba.
Saraki ya kara da cewa, ba zai yi mamaki ba,
idan har gwamnatin shugaba Buhari ta yi amfani da jami’an tsaro a zaben 2019,
ganin cewa ‘yan Najeriya sun yanke kyakkyawan fatan da suke yiwa gwamnatin mai
ci.
Shugaban majalisar dattijan ya ce a ra’ayinsa
kamata ya yi gwamnatin Najeriya ta maido da tallafin sauke farashin man fetur,
ta hanyar ware wa tallafin kasafi na musamman, domin baiwa bangaren ‘yan kasuwa
damar shiga sha’anin shigo da man fetur daga kasashen ketare.
A cewar Saraki, Najeriya tana bukatar
jagorancin shugaban kasa mai ra’ayin ciyar da fannin cinikayya gaba kuma wanda
zai iya daukar matakan nan take wajen shawo kan matsalolin tsaron da ke damun
sassan kasar.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku