MATAIMAKIN GWAMNAN JIHAR KANO HAFIZ ABUBAKAR YA AJIYE AIKIN MATAIMAKIN GWAMNA

A jiya Lahadi ne mataimakin gwamnan jihar Kano Hafiz Bello ya mika takardar ajiye aiki wato sauka daga kujerar mataimakin gwamnan jihar 
Kano.



Kakakin Hafiz, Abdulwahab Ahmad ne ya mika wa PREMIUM TIMES kwafin takardar.
A cikin takardar, Hafiz ya bayyana cewa sam baya jin dadin yadda suke aiki da gwamnan jihar Abdullahi Ganduje.
” Kwata-kwata gwamna Ganduje ba ya daraja kujera ta na mataimakin sa. Ko na bada shawara ba ya dauka da hakan yasa muka fada cikin kamayamayar da jam’iyyar ta shiga a yanzu a jihar.
” Na yi ta fama da bakin ciki, zaman maraici da kakanikayi duk a dalilin rashin daraja ni da kujerar da nike zaune a kai. A haka ne na yi shawara sannnan na yanke hukuncin hakura da aikin kawai.
Shi dai Hafiz Abubakar makusancin sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da ake ganin nan ba da dadewa ba zai canza sheka ya koma PDP.


DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/

ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html

Comments