MANYAN ‘YAN TAKARAR SHUGABAN KASA 5 DA SUKA ZIYARCI OBASANJO KWANAN NAN


A ‘yan kwanakin baya bayan nan tsohon shugaban kasa Obasanjo ya karbi bakuncin manyan ‘yan siyasar kasar nan dake burin yin takarar shugabancin kasa a zabe 2019.
Ga wasu daga cikin manyan manyan ‘yan takarar da suka ziyarce shi.



1.    ATIKU ABUBAKAR
A ranar 27 ga watan Yuli ne aka hangi Atiku da Obasanjo na gaisawa a wurin wani taro na kaddamar da cibiyar Gusau. Duk ba a ga maciji tsakanin mutanen biyu, ana ganin gaisawar ta su tamkar wata nuna amincewa ce Obasanjo ya nuna ga takarar Atiku.

2.     SULE LAMIDO
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ziyarci Obasanjo a ranar 7 ga watan Agusta inda suka shafe sa’a biyu suna tattaunawa.

3.     BUKOLA SARAKI
Tun bayan ficewarsa daga jam’iyyar APC ake rade-radin cewar Bukola Saraki zai tsaya takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP day a koma. A ranar 14 ga watan Agusta ne Saraki ya ziyarci Obasanjo a gidansa dake Abeokuta, babban birnin jihar Ogun kuna sun shafe kusan sa’a biyu, daga 5:27 zuwa 7:12, suna kus-kus.

4.     IBRAHIM DANKWAMBO
Gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo, ba a bar shi a baya ba wajen kaiwa Obasanjo ziyara. Dankwambo, gwamna mai ci a karkashin jam’iyyar PDP, ya ziyarci Obasanjo ne a ranar Laraba, 15 ga watan Agusta, a gidansa dake Abeokuta, jihar Ogun.

5.     TANIMU TURAKI
Tsohon minista a gwamnatin PDP ta shugaba Jonathan, Tanimu Turaki, ya ziyarci Obasanjo a gidansa domin shaida masa kudirinsa na son yin takarar shugaban kasa a zaben 2019.



Comments