KWARARRU NA DUNIYA ZA SU GANA KAN CETO TAFKIN CHADI


Yau ake saran kwarraru daga kasashen da ke amfani da tafkin Chadi har ma da wasu masana daga sassan duniya za su fara wani taro a birnin Abujan Najeriya domin shata dabarun ceto tafkin da ke ci gaba da tsukewa.





Wannan taron da zai janyo masana daga kasashen duniya da dama tare da wakilan Majalisar Dinkin Duniya, zai kunshi masana harkar samar da ruwa da kuma killace shi daga kasashen da suka mallaki tafkin da suka hada da Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi.
Bayan kwashe shekaru 10 ana fafatawa da mayakan Boko Haram da suka hana miliyoyin mutane daga wadannan kasashe amfana da tafkin ta hanyar noman rani da kamun kifi, wani taro da aka gudanar a kasar Chadi a watan Nuwambar bara, ya bada shawarar lalubo hanyar ceto tafkin da killace shi da kuma bunkasa shi yadda zai ci gaba da samarwa miliyoyin mutanen ayyukan yi da kuma dogaro da kai.
Taron na yau wani sharen fage ne na taron ministocin kasashen tafkin Chadi da zai gudana ranar 30 ga wata.
Cikin masu halartar taron na yau har da mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo da wakilin raya kasashe na Majalisar Dinkin Duniya, Dr. Samuel Bwalya da kuma wakiliyar Kungiyar Kasashen Afirka Amb. Hadiza Mustapha.

DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 


Comments