KOTU TA TABBATAR DA NASARAR MNANGAGWA A ZABEN ZIMBABWE


Babbar Kotun Zimbabwe yau Juma'a ta yi watsi da karar babbar Jam'iyyar adawar kasar tare da tabbatar da nasarar Emmerson Mnangagwa a zaben kasar na watan Yuli. Zaman kotun na yau ya ki amincewa da bukatar bangaren adawar da ke neman soke babban zaben kasar da ya nuna shugaba Emmerson Mnangagwa a matsayin wanda ya lashe bisa zargin tafka magudi a cikinsa.

Mai shari'a Luke Malaba da ya jagorancin karar a babbar kotun da ke birnin Harare ya ce babu cikakkun hujjoji da ke kare karar da babbar Jam'iyyar adawar ta MDC ta shigar.

Sai dai lauyoyin da ke kare Jam'iyyar ta MDC sun ce Jam'iyyar Mnangagwa ta ZANU-PF ta tilastawa masu kada kuri'a wajen zabenta.
Tuni dai Shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ya nemi hadin kan al'ummar kasar tare da kwantar da hankula ta wani jawabi da ya yi na kai tsaye a gidan talabijin mallakin kasar jim kadan bayan hukuncin na Kotu.
Jam'iyyar ZANU-PF dai ta yi nasara ne a zaben na Zimbabwe da kashi 50.8 a zaben na ranar 30 ga watan Yuli yayin da dan takarar bangaren adawa Nelson Chamisa kuma ya samu kashi 44.3
Ministan shari'ar kasar ta Zimbabwe Ziyambi Ziyambi ya ce za a rantsar da shugaba Mnangagwa ranar Lahadi mai zuwa.

 DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/

ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html

Comments