IGP YA SAMU UMURNIN KOTU KAN AIKA SAMMACI GA SARAKI


Sufeto janar na yan sanda, Ibrahim Idris ya samu damar aika sammaci ga shugaban majalisar dattawa akan fashin Offa.




A wata wasika daga Barista Oliwatosin Ojaomo ya aika ga sufeto janar na yan sanda ya nemi a aika sammacin gaggawa ga shugaban majalisar dattawa kamar yadda sashi na 122 na dokar laifi na 2015 ya tanadar. An bayar da damar ne a ranar 31 ga watan Yuli daga kotun Grade One Area Court, ACO Estate, Lugbe, Abuja dauke da lambar shari’a : CR/196/18 tsakanin Ojaomo da Bukola Saraki.

Lauyan ya zargi Saraki, wadda yaki amsa gayyatar IGP a ranar 24 ga watan Yuli, 2018, “da kawo cikas wajen gudanar da biciken laifi sannan ya ki mutunta jami’in gwaamnati wadda ke gudanar da aikin doka” hakan kuma laifi ne a sashi na 136 da 149.




DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/

ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html

Comments