HANKULAN SHUGABANNIN SIYASA BAI KWANTA DA GWAMNATIN BUHARI BA - OKOROCHA
Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya bayyana
cewa hankulan shugabannin siyasa a kasar bai kwanta da gwamnatin shugaban kasa
Muhammad Buhari ba don haka suka hade masa kai.
Gwamnan wadda ya kara da cewa shugaban kasar
bai aikata aibu a garesu ba, ya bayyana cewa shugabanni na tsoron a hukunta su
akan rashawar da suke yi hakan ne yasa suka hadewa shugaban kasar kai.
Gwamnan yace shugaban kasar ya yarda da al’umma
sannan kuma ya yarda cewa dole a yi taka tsantsan da arzikin kasar don jama’a
su amfana daga gare shi, inda ya kara da cewa wadannan dalilai ne yasa
shugabannin suke ganin bakin Buari sannan suna aikata hakan ne domin son
zuciyarsu.
Gwamnan ya kara da cewa ya zama dole yan
Najeriya su marawa shugaba Buhari baya domin yayi korari sosai wajen tsayawa
kan gaskiya kuma bai amince da yin almubazaranci da dukiyar jama’a ba.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku