GWAMNATIN KANO ZA TA DAUKI MALAMAI MATA 1,196 A JIHAR



Gwamnatin jiha Kano ta bada umurnin daukan malamai mata 1,196 da ke da kwalin kwalegin ilimi a fadin jihar.



Kwamishanan matasa, raya al’adu da yada labarai na jihar, Muhammad Garba, ya bayyana hakan ne a hira da manema labarai a jihar.

Gwamnatin jihar ta Kano ta umurci ma’aikatar ilimin kananan hukumomi wato Local Government Education Authority (LGEA) ta shirya takardun daukan aikin wadanda aka dauka da kuma sanya sunayensu cikin asusun albashin gwamnati.

A bangare guda, makarantan horas da malamai wato National Teachers Institute NTI ta bada umurnin amfani da kudi N450m wajen horas da malaman ilimin lissafi da kimiya 500. 

A cewarsa, wannan wani mataki ne da gwamnatin jihar ke dauka wajen inganta ilimi da kuma tabbatar da cewa jihar Kano na an gaba. Kana zai karfafa mata ta hanyar samar musu aikin yi a ma’aikatar ilimin jihar.



DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 

Comments