GWAMNATI TA CIYO BASHIN DALA MILIYAN 150 DON KAWAR DA CUTAR SHAN INNA A NAJERIYA
Ministan harkokin Kudi Kemi
Adeosun ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ciyo bashin dalla miliyan 150 daga
bankin duniya domin kawar da cutar shan inna.
Kemi ta sanar da haka ne bayan
kammala taron kwamitin zartaswa da mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya
shugabanta a makon da ya gabata.
A
bayanan da ta yi Kemi ta ce gwamnati za ta yi amfani da wannan kudade ne wajen
siyo maganin rigakafin da za a yi amfani da shi wa yara.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne Gwamnatin Najeriya ta kara tabbatar wa ‘yan Najeriya shirinta na ganin cewa ta kawar da cutar shan inna a kasar ta hanyar wadatar da jihohin kasar nan kudade domin kawo karshen cutar.
Mataimakin shugaban kasa Yemi
Osinbajo wanda ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da hakan a
taron da aka yi don samar da mafita kan hakan.
Osinbajo
ya ce cutar shan inna ta sake bullowa ne bayan kasa Najeriya ta yi shekaru uku
ba’a sami sanarwan sake bullowar ta ba.
Ya
ce hakan ya faru ne saboda aiyukkan kungiyar Boko Haram da ya hana ma’aikatan
rigakafin cutar shiga wasu garuruwa a yankin.
Ya
kuma ce gwamnatin Najeriya za ta wadata jihohin da duk kudaden da suke bukata
domin kawar da cutar gaba daya a kasa Najeriya.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku