DALILIN DA YASA INEC BA ZATA DAGA ZABEN 2019 BA

Hukumar zabe mai zaman kanta na kasa INEC tace ba zata dage babban zaben shekarar 2019 ba kawai saboda an samu jinkiri wajen amincewa da kasafin kudin hukumar.


Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya bayyana hakan a yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai daga gidan gwamnati a ranar Juma'a a Abuja. Ya ce babu kudin tsarin mulki bai bayar da ikon dage zaben ba saboda haka ba zai yiwu a dage zaben ba.

"Kamar yadda na saba maimaitawa, babu wani dalili da zai hana a gudanar da zabe a cikin dokar zabe na kasa mai lamba 26 dake kundin tsarin mulki. "Mun tsayar da ranar zaben, za'a fara a ranar 16 ga watan Fabrairun 2019; mun fitar da jadawalin zaben kafin zaben yazo, wannan shine karo na farko da hakan ta faru a tarihin Najeriya. Jama'a sun san lokacin da za'a fara zaben shekara daya kafin fara zaben."


DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/

ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html

Comments