BUHARI YA DAWO NAJERIYA BAYAN KAMMALA HUTUNSA A LONDON



Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya bayan gajeren hutu na kwanaki 10 da ya yi a birnin London na Birtaniya. Shugaban ya samu tarbe daga mukarraban gwamnati dama dubban masu goyon bayansa a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke babban birnin kasar Abuja.

Saukar Shugaba Muhammadu Buhari A Filin Jirgin Nnamdi Azikwe a Abuja

Tun a ranar 3 ga watan Agusta, 2018, shugaban ya fara hutun kwanaki 10 a birnin London inda mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ya ci gaba da tafiyar da al’amuran kasar a matsayi mukaddashin shugaba.
Daga cikin muhimman ayyukan da mataimakin shugaban Najeriyar, Farfesa Yemi Osinbajo ya zartar akwai sauya shugabancin hukumar jami’an tsaron farin kaya ta DSS, inda ya maye gurbin Lawal Daura da Mista Matthew Seiyefa.
Korar Lawal Daura daga mukaminsa ya biyo bayan umarnin da ya baiwa jami’an hukumar ta DSS na datse kofar shiga majalisun Najeriya a farkon watan Agusta , lamarin da haifar da ce-ce-ku-ce a ciki da wajen kasar.
Farfesa Osinbajo, ya kuma bada umarnin sauya fasalin shugabanci da ayyukan rundunar ‘yan sandan kasar ta musamman mai yaki da fashi da makami da sauran manyan laifuka wato SARS.
Umarnin yi wa rundunar garambawul ya biyo bayan koken jama’a da ya yawaita, kan yadda jami’an ‘yan sandan da ke karkashin rundunar ta SARS ke cin zarafin mutane yayin gudanar da ayyukansu.


DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/

ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html

Comments