BOKO HARAM TA KASHE SOJOJIN NAJERIYA TA KUMA SACE MAKAMAI



Akala sojojin Najeriya 17 mayakan Boko Haram suka hallaka a wani sabon hari da suka kai wani sansanin sojojin a yankin Arewa maso gabashin kasar.





Wata majiya ta jami'an tsaron ta sheidawa kamfanin dillancin labarai na Faransa cewa a ranar Alhamis mayakan Boko Haram sun yi awon gaba da makamai, tareda kashe sojojin Najeriya, yayinda wasu suka bata a wannan harin da ya kasance na uku a kasa da wata guda.
A makon da ya gabata dai ne rundunar sojin Najeriya ta sanar da damke wani kwamandan kungiyar Boko Haram da ta shafe lokaci mai tsawo tana neman sa ruwa a jallo.



DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/

ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html

Comments