BABBAR SALLAH: GWAMNATIN TARAYYA TA BAYYANA RANAKUN HUTU


Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun Talata, 21 ga watan Agusta, da Laraba, 22 ga watan Agusta a matsayin ranakun hutu domin murnar babbar salla (Eid-el-Kabir).



Ministan harkokin ciki gida, Abdulrahman Dambazau, ne ya sanar da hakan yau, Alhamis, a Abuja a wata sanarwa da Umar Mohammed, babban sakataren ma’aikatar ya sakawa hannu.


Gwamnatin tarayya ta taya ‘yan Najeriya murnar zagayowar babbar sallar tare da yi masu fatan yin bukukwan sallah lafiya. Kazalika, gwamnatin ta bukaci ‘yan Najeriya su rungumi soyayya da kaunar juna domin samun zamana lafiya mai dorewa, kamar yadda Dambazau ya sanar.


Dambazau ya bukaci ‘yan Najeriya dake gida da kasashen ketare das u cigaba da bawa gwamnatin shugaba Buhari hadin kai musamman a kokarinta na tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a tsakani jama’a.



DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 

Comments