AN SAMU KARUWA A INGANCIN KIWON LAFIYA A NAHIYAR AFIRKA


Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta sanar cewa an samu karuwa a ingancin kiwon lafiyar da ake samu a yankin kasashen nahiyar Afrika.

WHO ta bayyana haka ne a taro da aka yi Dakar kasar Senegal.
” Yankin Afrika za ta iya samu ci gaba a fannin kiwon lafiya ne idan gwamnatocin kasashen sun ware isassun kudade domin shawo kan yaduwar cututtuka da suka addabi mutanen yankin.
” Sannan asibitocin kasashen su kara mai da hankuli su wajen kula da kiwon lafiyar musamman matasa da tsofaffi.
A karshe jami’ar WHO Matshidiso Moeti a nata tsokacin ta bayyana cewa inganta fannin kiwon lafiya a kasashen Afrika shine mafita ga matsalolin da ake fama da su a nahiyar gaba daya.



DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA  

Comments