AN HANA DOGARA YIN ZABE A BAUCHI


Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara ya tausa matasan mazabar sa bayan hana su kada kuri’a da aka yi a zaben Bauchi.

Jiya Asabar ne aka gudanar da zaben cike gurbi na kujerar sanatan da zai wakilci shiyyar Bauchi ta Kudu a majalisar Dattawa.
Shi kan sa Dogara an hana shi kada kuri’a wai shima yayi lattin zuwa.
Sai dai kuma an rufe zabe a mazabar Yakubu Dogara ne tun karfe 2:20 na rana inda daga nan babu wanda aka yarda ya jefa kuri’a.
Abin da ya kai ga wasu daga cikin masu zabe suka tada husuma a wannan mazaba.
Da yawa daga cikin su sun koka cewa sai da suka tafi gonakin su kafin nan suka zo rumfunar zaben.
Sai dai duk da haka ba a yarda sun yi zaben ba.


DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/

ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html

Comments