AMNESTY TA BUKACI KAWO KARSHEN KAME BA BISA KA'IDA BA A NAJERIYA


Kungiyar kare Hakkin Bil Adama ta Amnesty International ta zargi gwamnatin Najeriya da kama mutane ta na tsarewa da kuma batar da su ba tare da kai su gaban shari’a ba.
Sanarwar kungiyar ta ce gwamnatin Najeriya na amfani da matakin wajen rufe bakin yan adawa da kuma tilasta tsoro kan fararen hula.

Daraktan kungiyar Osai Ojigho ta bada misali da kama wani dan jarida Abiri Jones da hukumar DSS ta yi, wanda gwamnatin ta ki amincewa har sanda aka kwashe shekaru 2 ana tsare da shi.
Kungiyar ta kuma bukaci gwamnatin Najeriya ta yi bayani kan tarin mutanen da ake zargin cewar ta batar da su, cikin su harda mabiya Shia’a kusan 600.


DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA  

Comments