AKWAI FARGABA DANGANE DA TSARO A AREWA MASO GABASHIN NAJERIYA



A Najeriya rahotanni kan tsaro daga yankin arewa maso gabashin kasar na haifar da shakku matuka a cewar gwamnatin tarayyar kasar.

Ministan tsaron kasar Mansur Dan Ali, ya shaida wa manema labarai bayan taron da shugaban kasar Mahammadu Buhari ya jagoranta da shugabannin rundunonin tsaro cewa, tabbas an samu cigaba ta fannin tsaro musamman a jihohin Benue, Zamfara da kuma yankin Niger Delta, to sai dai ba haka lamarin yake ba a yankin arewa maso gabashin kasar.

Ministan ya ce taron ya dauki wasu tsauraran matakai domin tunkarar wannan matsala ta tsaro da ake fuskanta a yankin.


Comments