AISHA BUHARI ZATA KARBO DIGIRIN GIRMAMAWA A KASAR KORIYA


Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta isa birnin Seoul na kasar Koriya gabanin bikin karrama ta da digirin girmamawa da jami'ar Sun Moon zata yi a yau Litinin 13 ga watan Agusta.

Farfesa Hong Young-Shik na sashen karatun kimiyyar siyasa ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis yayin wata ziyara da suka kaiwa Aisha Buhari a fadar gwamnatin tarayya.

"Zamu karrama Aisha ne saboda irin aiyukan taimakon jama'a da take yi musamman ta fuskar inganta rayuwar mata da kananan yara," a cewar Farfesa Hong.


DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/

ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html

Comments