AHMAD BABBA-KAITA NA JAM’IYYAR APC YA LASHE ZABEN SANATA A KATSINA
Dan takarar kujerar Sanata na
jam’iyyar APC, Ahmad Babba-Kaita ya lashe zaben cike gurbi da aka gudanar
ranara Asabar a Katsina.
Kamar yadda aka bayyana sakamakon,
Ahmad Babba-Kaita ya sami kuri’u 224,607 sannan Wan sa, da tsohon ma’aikacin
kwastam ne, kuma dan takara na jam’iyyar PDP Kabir Babba-Kaita ya sami kuri’u
59,724.
Hukumar
Zabe mai zaman kanta ta bayyana cewa cikin mutane 855,092 da suka yi rijista,
sama da mutane 300,000 ne aka tantance a rumfunar zabe dake wannan shiyya.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku