ABOKI YA GUNTULE MA ABOKINSA HANNU BAYAN FADA YA KAURE A TSAKANINSU SABODA BUDURWA
Rundunar
Yansandan garin Zuba dake babban birnin tarayya Abuja ta kama wani matashi mai
suna Yusuf Hassan inkiya Dakwa wanda ake zarginsa da sare ma abokinsa hannu mai
suna Abubakar Umar, inji rahoton Aminiya.
Rikicin ya kaure ne a tsakanin matasan akan
wata budurwa da guda daga cikinsu ke so, inda a wannan rana na Dakwa ya bi
Abubakar har gida, inda ya bukaci ya fito su dambace, fitowarsa keda wuya ya
kai masa sara.
Sai dai Abubakar ya bayyana cewa yarinyar da
ake rikici akanta ta fito ne daga jihar Kaduna tare da mahaifiyarta inda suka
zo garin Zuba don gudun hijira sai dai basu samu wajen zama ba, hakan ya say a
basu dakinsa dake cikin gidansu, shi kuma ya koma ya tare a dakin abokinsa
Dakwa.
Ana cikin hakan haka ne sai Dakwa ya fara
soyayya da yarinyar, amma bayan kwana biyu sai ya fara zargin wai Yusuf yana
neman yarinyar shi ma, wannan dalilin da ya haifar da rashin jituwa a
tsakaninsu, har ta kai ga amincin ya lalace kuma Dakwa ya fara yi ma Yusuf
barazana. Wadanda suke da masaniya game wannan tirka tirka sun tabbatar da
cewar akwai lokacin da Dakwa ya kwaso wasu yan daba guda biyar da nufin su
kassara Yusuf a yayin da yake gona tare da mahaifinsa, amma yan daban suka yi.
Har sai ranar da yazo gidansu Yusuf yana ta zage zage wai ya fito suyita ta
kare, “Dana fito ne sai ya dauke adda ya kai mani sara a wuya, ni kuma na kare
da hannuna, nan take hannun ya guntule, shi kuma a yayi kokarin tserewa, amma
matasan unguwa suka kama shi.” Inji Yusuf. Kaakakin Yansandan yankin, CSP
Fodiyo Sani ya tabbatar da faruwar lamatin, inda yace zasu gurfanar dasu gaban
Kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku