2019: AN CEWA DANKWAMBO YA HAKURA YA BARWA TAMBUWAL TAKARA


Alamu sun nuna a jiya cewa an sanyawa gwamnan jihar Gombe kuma dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin lemar Peoples Democratic Party (PDP), Ibrahim Hassan Dankwambo, zafi cewa ya hakura da kudirinsa gabannin zaben fid da gwani na jam’iyyar.




Jaridar NAIJ.com ta tattaro cewa Dankwambo waanda ya bayyana kudirinsa na son takarar shugaban kasa makonni biyu da suka shige na fuskantar matsin lamba daga wasu shugabannin siyasa da sarakuna a yankin arewacin kasar kan ya hakura ya barwa gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal. Ku tuna cewa Tambuwal, wanda ya kasance tsohon kakakin majalisar wakilai na daya daga cikin manyan yan siyasan da suka sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa PDP a kwanan nan.



Bincike sun nuna cewa dalilin zabar Tambuwal ya kasance saboda yakinin cewa yana da dunbin magoya baya a fafutukar fiye da Dankwambo. Majiyoyi na kusa da gwamnan sun fadawa majiyarmu ta Leadership cewa sakamakon matsin lamba da yake samu da kuma goyon bayan da aka ba Tambuwal a yanzu, Talban Gomben na duba ga neman takarar kujerar sanata na Gombe ta arewa.




Comments