ZABEN JIHAR EKITI: ‘YAN SANDA SUN KAMA WASU ‘YAN PDP DA DANGWALALLUN KURI’UN ZABE
Yayin day a rage saura kwanaki hudu a yi zaben
gwamna a Ekiti, hukumar ‘yan sanda a jihar ta kama wasu ‘yan jam’iyyar PDP da
kuri’un da aka kamala dangwale su. Dukkan kuri’un an dangwalawa PDP ne.
A wani rahoto da Mista Wole Olujobi, Darektan
yada labarai na kamfen din Kayode Fayemi, dan takarar APC, ya fitar ya bayyana
sunayen mutane biyun da aka kama; Ashiru Gbenga da Olaide Olayeye. Yanzu haka
suna bawa jami’an ‘yan sanda muhimman bayanai dangane da kuri’un da aka kama su
da su.
Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Ekiti,
Mista Caleb Ikechukwu, ya yi alkawarin samar da Karin bayani ga jaridar The
Nation bayan sun nemi jin ta bakinsa a kan lamarin.
Rahotanni sun bayyana cewar da misalign karfe 12:00 na rana ne aka sanar
da hukumar ‘yan sanda ganin wata mota kirar Vien Foton mai dauke da lamba KTU
477 DG da ta zo daga Legas a ajiye a kasuwar Fayose dake kan titin Ajilosun a
Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti. Zargin wurin da aka ga motar ne ya saka
jami’an ‘yan sanda suka fara bincikenta kuma daga bisani suka gano kuri’un da
aka zo da su a dangwale a cikin motar.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku