ZA’A KASANCE CIKIN MATSANANCIN DUHU A NAJERIYA RANAR JUMA’A SABO DA ZAZZABIN WATA – MASANA KIMIYYA




A daren gobe, Juma’a, ne ake zaton samun nusanin wata da ba a taba fuskantar irinsa ba a tarihin Najeriya, kamar yadda Farfesa Augustine Ubachukwu, na bangaren ilimi da binciken sanin sararin samaniya a jami’ar Najeriya dake Nsukka ya sanar.




Farfesa Ubachwukwu, wanda ya kasance shugaban sashen bincike da ilimin sanin sararin samaniya, ya sanar da hakan ne yau, Alhamis, a Abuja yayin wata ganawa day a yi da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN). “Najeriya zata fuskanci zazzabin wata a ranar juma’a, 27 ga watan Yuli. Za a samu daukewar hasken farin wata daga karfe 9:30 na dare har zuwa karfe 11:22,” a cewar Farfesa Ubachukwu.

Farfesa ubachukwu ya kara da cewar wannan shine zazzabin wata mafi tsawo da za a gani a karon farko tun bayan wasu shekaru daruruwa da suka wuce kuma zai shafi sassann duniya da suka hada da Turai, Afrika, Asia, Australia da New Zealand. A cewar Farfesa Ubachukwu, zazzabin wata ba kamar na rana ne, a saboda haka jama’a kan iya ganinsa da idonsu ba tare da amfani da gilashin kare idanu ba.

Masanin ya bayyana cewar bayan wannan zazzabin watan, Najeriya zata kara fuskantar irinsa a watan Janairu na shekarar 2019. Wani masanin ilimin sararin samaniya, Farfesa Rabi’u Babatunde, na cibiyar binciken sararin samaniya dake jihar Kogi ya bukaci jama’a da kada su damu da zazzabin da watan zai yi domin hakan na daga cikin shaidar cewar duniyar mu ba a tsaye take wuri guda ba, wato tana motsi ko a ce juyawa.



DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com

Comments