'YAN SANDA SUN YI ZANGA ZANGA A MAIDUGURI
Jami'an 'yan sanda a jihar Borno sun mamaye titunan Maiduguri, babban birnin jihar Borno a yau (Litinin) a cikin wata zanga-zanga da suke yi.

Jami'an sun yi zanga-zangar ne dangane da kudaden su na watanni shida da
ba ‘a biya sub a. Sun yi ta zanga zangar ne a manyan tituna da ke kusa da
hedkwatar 'yan sanda a jihar.
Mazauna yankin sun shaida wa gidan talabijin na Channels cewa, jami'an
sun yi ta harba bindigogi a sama, inda hakan ya kawo firgita ga mazauna yankin,
har wadansun su suka nemi mafaka.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku