‘YAN SANDA SUN KAMA MUTANE BIYAR BISA ZARGIN BUGA JABUN DALOLI
Kwaminshinan ‘Yan sandan jihar Gombe,
Shina Olukolu, ya tabbatar da cafke wasu mutane biyar bisa zargin laifin buga
takardun kudaden jabu na dalolin Amurka.
Ya ce masu damfarar sun yi amfani da
yanzu ne lokacin da ake hada-hadar tafiya aikin Hajji da niyyar su rika
damfarar maniyyata.
An kama su ne da daloli guda, ‘yan
dari-dari.
Kwamishinan ya kara da cewa an kama
biyu daga cikin wadanda ake zargin da dala 200, bayan da suka gayyaci wani mai
suna Tamin Idris daga Legas, suka ce ya je Gombe, domin ba shi canjin dala.
Daga nan sai ya gargadi maniyyata da
su guji canjin dala daga mutanen da suke da shakku ko kuma wadanda suke canjin
kudaden waje ba bisa ka’ida ba.
Ya ja kunnen cewa duk wanda ya shafa musu mai ga bakin cewa zai saida
musu dala a arha bagas, to dan damfara ne.DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku