YAN FASHI DA MAKAMI SUN YI MA YANSANDA 2 TUMBUR




Wasu jami’an Yansandan kasar Kenya sun gamu da wulakanci na karshe daga wajen wasu gungun yan fashi da makami a garin Nairobi, babban birnin kasar, inda suka cire musu kaya, tsirara haihuwar uwarsu sa’annan suka kwace musu kudi da wayoyi.
Jaridar Punch ta ruwaito wannan lamari ya faru ne akan babban hanyar Nakaru-Nairobi a daren Litinin, 2 ga watan Yuli, inda Yan fashin suka shigar da mutanen dake cikin wata mota cikin dajin Kinale.
Majiyar ta ruwaito wasu daga cikin fasinjar motar da Yansandan suke ciki ne suka umarci direban motar da ya tsaya zasu sauka da misalin karfe 9 na dare, amma yayin da suka tsaya sai kwatsam yan fashin suka bayyana, inda suka shigar dasu dajin, suka kwantar dasu, sa’annan suka kwashe yan kudadensu.
Wani daga cikin Fasinjojin Motar, Abraham Karani ya bayyana cewa: “Muna cikin kwashe kayanmu daga motar kenan, sai ga yan fashin sun bayyana dauke da bindigu, inda suka kwace motar har suka kai mu wani daji, sun kwashe awanni suka dukanmu tsirara, tare da kwashe mana kaya.” Shima Kaakakin rundunar Yansandan yankin Naivasha, OCPD Smuel Waweru ya tabbatar da faruwar laamarin, inda yace sai da misalin karfe hudu na Asubah aka ceto mutanne, inda aka garzaya dasu caji ofis don karbar bayanansu. “Mun mayar da aikin binciken lamari zuwa ga ofishin Yansandan Lari, saboda a can ne aka yi wannan laifi, kuma muna da tabbacin zasu kama duk masu hannu cikin wannan lamari.” Inji shi.



Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta

Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com

Comments