YAKI DA CUTAR KANJAMAU
Masana kimiya sun bayyana samun koma-baya a yunkurin samar da maganin cutar kanjamau a taron duniya da yanzu haka ke gudana a Amsterdam, abin da ke nuna fargabar samun maganin cutar da kuma illar da take yi wa jaririn da aka haifa.
Wani rahotan binciken da aka gabatar wajen taron na 22, ya bayyana samun matsaloli guda 4 daga cikin haihuwar da mata 426 da ke dauke da cutar suka yi a kasar Botswana sakamakon amfani da maganin ‘dolutegravir’ kafin daukar ciki.
Sakamakon binciken ya ce, matsalar da dan-tayi kan samu idan aka yi amfani da maganin, na haifar da illa ga kwakwalwar jariri ko kuma kashin-bayansa a makwannin farko bayan daukan ciki wanda ke haifar da bari.
Rebecca Zash ta Jami’ar Havard ta ce, an gano matsalar ne a binciken da aka gudanar tsakanin watan Agustan shekarar 2014 zuwa Mayun bana.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com

Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku