WANI DAN SHEKARU 20 YA KASHE KANSA ‘A INDIA



Wani matashi mai shekaru ashirin (20) ya rataye kansa ‘a India.
Rahotanni sun bayyana ta wata majiya a yanar gizo cewa Lamarin ya faru ne bayan da kasar Faransa ta doke Argentina daga wasan kwallon kafa na gasar cin kofin duniya 2018 a Rasha.
Matashin wanda aka shaida shi da suna Halder ya kashe kansa ne a garin Habibpurda ke yammacin Bengal’s Malda a India, ganin cewa shi masoyin dan wasan kwallon kafan nan da yayi suna a wasan kwallon kafa (Messi). Bai zaci cewa Argentina zata iya komawa gida ba, tsantsan bacin rai da tashin hankali, bai yi jinkiri ba, sai ya shiga dakin say a kulle kofarsa da safiyar ran Lahadi inda aka yi yunkurin bude kofarsa amma kash, bayan da ‘yan sanda suka balle kofar tasa sai suka iske shi ya riga ya bakonci kiyama, gangan jikin sa tana lilo a sama da igiyar da ta shake shi har sai da ya daina numfasawa.



Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta


Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com

Comments